Dawood dai bafullace ne da ya gaji Shanu 40 daga gurin mahaifinsa a asalin karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, yace aikin soja da ya kaishi Maiduguri da wasu sassan Najeriya sun sa shi gano barin yara na gararanba kan tituna ne a karshe kansa zuciyarsu ta kekashe su fada aikin ta’addanci.
Jami’an sojan Ruwa da malaman jami’a ne suka taru a kwalejin koyar da dabarun yaki a Abuja don kaddamar da littafin. Dawood ya bada shawarar kafa dokar hana yara gararamba kan tituna, ko kuma a hana tura su almajiranci.
Kwanakin baya a Abuja kungiyar JIBWIS ta kaddamar da wani littafi mai take ‘daya da wannan, inda Sheik Hamza Adamu Abdulhamid, ke cewa ya zama wajibi a nemi ilimin addni da Boko da zama lafiya tare.
Jikan Sardauna Hassan Dan Baba Magajin garin Sokoto shine ya kaddamar da littafin, wanda har ila yau ya kunshi kyawawan al’adun Fulani dake nuna kiwon Shanu baya hana neman ilimi.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.