Mataimakin shugaban kasar, wanda yace kubutar yaran abin yabawa ce, ya musanta rahottanin dake cewa “ba ni gishiri, in baka manda” aka yi tsakanin gwamnati da ‘yan Boko Haram, inda aka saki wasu kwamandoji hudu na BH din kafin su kuma su sako ‘yan matan.
Shima ministan watasa labaran Nigeria Lai Mohammed ya dora nasarar samo ‘yanmatan akan abinda ya kira “cijewar da aka yi wajen gudanarda tattaunawa da sulhuntawan da suka haifar da aminci” ne a tsakanin saassan biyu (gwamnati da BH.)
Rahottani sunce kungiyar bada agaji ta Red Cross da gwamnatin kasar Switzerland ne suka jagoranci tattaunawar da ta kai aka sako ‘yanmatan, kuma hukumomin na Nigeria sunce za’a ci gaba da tattaunawar don neman kubutar da sauran ‘yanmatan da suka rage a tsare a hannun ‘yan BH.
Tun a watan Afrilun 2014 ne dai mayakan BH suka yi awon gaba da ‘yanmatan su kusan 300 daga wata makarantar sakandare dake garin na Chibok a jihar Borno. Da yawansu sun samu sun gudu, amma dai har yanzu akwai 219 a tsare.