Kungiyar tayi murnar sako 'yan mata 21 a karon farko tunda aka sacesu fiye da shekaru biyu da suka gabata, a wannan karon ne suka fi yawa.
Sako 'yan matan ya kawarwa kungiyar ta Bring Back Our Girls zargin cewa gwagwarmayar da su keyi domin a sako 'yan matan aikin babangiwa ne. Wasu ma sun ce shiri ne kawai domin kawar da gwamnatin Jonathan.
Abun da ya fito fili yanzu shi ne tasirin kungiyoyi musamman ma kungiyar nan ta agaji ta Red Cross dake shiga tsakanin bangarori biyu masu hamayya da juna, a yi bani gishiri in baka manda.
Shugaban kungiyar Red Cross dake Gombe Abubakar Yakubu ya bayyana irin yadda suke cimma irin wannan yarjejeniyar. Manufar kungiyar ita ce ta taimakawa dan Adam saboda idan mutum ya jikata sun samu damuwa. Koda kasashen da basa ga maciji tsakaninsu kamar Koriya ta Kudu da ta Arewa, Red Cross na shiga tsakaninsu ba tare da fallasa asirin kasashen wa junansu ba.
Akan ko dagewar kungiyoyin ne ya kaiga wannan nasarar, jigo a jam'iyyar APC mai mulki Hajiya Binta Muazu tace ba haka ba ne. Tace shugabannin sojojin yanzu jarumai ne wadanda basu da kwadaya illa dai cigaban kasa. Kasar ce ta damesu ba abun duniya ba. Tace kungiyoyi irin su Red Cross da kasar Switzerland da wasu da basa son a ambaci sunayensu suka shiga tsakani har aka sako 'yan matan 21.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.