Kungiyar ta bayyana cewa akwai bukatar shugaban Kasan Najeriya Muhammadu Buhari da yayi ahuwa ga sojojin nan 54 da aka yankewa hukunci daban-daban, wadanda kuma yanzu haka suke zaman gidan yari a gidajen yarin dake birnin Lagos daban-daban.
Kungiyar tace idan dai har gwamnati zata kame wasu manyan jamiaan gwamnatin da ta shude tare da zargin su da karkata kudaden makamai da yakamata ayi anfani dasu wajen yaki da kungiyar boko haram, don haka bata dalilin da zaisa a garkame wadannan sojojin ba matasa masu jini a jiki da suka yi kukan ba ‘ayi musu adalci ba wajen tura su fagen yaki ba tare da makamai ba.
Comrade Abubakar Abdulsalam shine shugaban wannan kungiyar ga abinda yake cewa.
‘’Abinda yasa dole mu daga murya mu tunatar da shugaban kasa game da batu yaran nan, domin ko wadannan yaran mara sa karfi ne kuma sun fito daga gidaje mara sa karfi, na biyu wadannan yaran sunyi kuka domin na ziyarci inda ake tsare da wadannan yaran a gidan yarin kiri-kiri, dana Ikoyi, da kuma hursuna matsakaici duka dake cikin birnin Ikko, Yaran sun nuna cewa anyi musu wannan hukuncin ne domin sun bukaci a basu wadattun makamai domin su huskanci abokan gaban su, a bisa wannan ne hukumar rundunar sojan Najeriya ta yanke musu wanmnan hukuncin shekaru goma-goma akan ko wane mutum guda, har su 54.
Sai dai rundunar sojan ta Najeriya tace bata da hannu a wannan hukuncin da aka yanke wa wadannan yaran.
Ga Babangida Jibrin da Karin bayani 2’59