Dangane da sako wasu 'yan matan Chibok su ishirin da daya jiya, Muryar Amurka ta zagaya birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo domin jin ra'ayoyin mutane akan lamarin.
Wani Muhammad Mai Agogo yace sun ji dadi da aka gano wasu cikin 'yan matan ba don komi ba domin wasu na ganin shi ne zai kawo zaman lafiya. Ya yiwu idan aka matsa ana iya sako sauran ma. Wadannan ma sai da aka saki wasu 'yan Boko Haram kafin su sako 'yan matan.
Mai Agogo yace amma Najeriya tayi takatsantsan da wadanda ake saki. Yace ina za'a ajiyesu ganin sun kashe mutane da yawa. Wadanda 'yan Boko Haram din suka kashe wa 'yanuwa za'a samu matsala dasu.
Hassana ta yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari farin ciki. Tace a lokacinsa ne aka soma yaki gadan gadan da 'yan ta'adan har ma gashi an soma gano 'yan matan.
Wani yace yayi murna an samu 'yan matan amma kada ace su kadai ne ake nema domin akwai mata da yawa daga jihohi daban daban dake hannun 'yan ta'adan.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.