Gwamnatin Najeriya ta ce al'ummar yankin dake fama da rikicin Boko Haram sun tabbatar da bayanan da aka samu a game da usulin Bashir Mohammed mai amfani da sunayen da suka hada da Abubakar Shekau, Abacha Abdullahi Geidam, Damasak, da wasunsu. An kashe Bashir a wani fadan da aka gwabza kwanakin baya a kusa da Maiduguri. Haka kuma, rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu mayakan Boko Haram su 135 sun mika kawunansu da makamansu ga hukumomi a yankin karamar hukumar Biu, dake Jihar Borno. Guda 88 sun yi saranda a Mairiga/Buni-Yadi, wasu 45 kuma a tsakanin Mubi da Michika.
Gwamnatin Najeriya Ta Ce Mohammed Bashir, Wanda Ke Amfani Da Sunan Abubakar Shekau, Ya Mutu, 25 Satumba, 2014

5
Hotuna biyu dake kokarin nuna kamanni a tsakanin gawar Mohammed Bashir da aka kashe da kuma hoton da aka cire daga bidiyo na mutumin dake kiran kansa Abubakar Shekau shugaban Boko Haram.

6
Wasu mayakan Boko Haram da suka yi saranda ga sojojin Najeriya suka mika makamansu a kusa da Maiduguri.