Sama da maharan 'yan Boko Haram talatin ne suka mutu a garin Madagali bayan wani fada da ya barke a tsakaninsu bisa ga sabanin ra'ayi akan bukatar su tsagaita wuta kuma su mika makamansu ga hukumomin Najeriya ko kuma a'a.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa 'yan bindigan sun ta yin harbe-harbe tsakaninsu yayin da wutar rikicin shugabanci ke kara ruruwa cikin kungiyar a yankin Madagali kamar yadda wadanda suka tsere daga yankin suka bayyana.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
Da alama sun rabu biyu yayin da wasu suke fada akan shugabanci wasu kuma suna fada akan sai su ajiye makamansu. Banda fadan da suke yi suna kuma fama da karancin man fetur a motocinsu. To sai dai abun mamaki har yanzu su 'yan Boko Haram din ne ke cigaba da rike Madagali da Michika duk da nasarorin da sojojin Najeriya suke ikirarin samu kwana kwanan nan.
Har yanzu al'umman yankin suna jeji wasu kuma suna Mubi ko Yola. Sojoji basu isa Michika ba ko Madagali.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.