'Yan Najeriya dake gudun hijira a kasar Kamaru suna gap da fadawa cikin yunwa domin karewar abincin dake hannunsu.
Yawancin 'yan gudun hijiran dake garuruwan Fatakol da Janabe da kuma Magashi sun shiga kasar ta Kamaru ne sakamakon hare-haren da 'yan Boko Haram suke kai masu.
Mafi yawan 'yan gudun hijiran sun fito ne daga jihar Borno da kuma wani bangare na jihar Adamawa da suka tagayyara sun fice daga jihohinsu ne sabili da rashin samun wani doki daga mahukuntan jihohinsu ko na gwamnatin tarayyar Najeriya.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
'Yan gudun hijirar da suka fito daga kananan hukumomin Gamboru-Ngala da Gwozah da Bama duk a jihar Borno da Michika ta jihar Adamawa sun fantsama ne zuwa kasar Kamaru domin neman tsira da ransu domin basu iya shiga manyan garuruwan jihohinsu ba sun fi kusa da Kamaru.
Yanzu dai sun kwashe fiye da wata guda a sansanoni na gudun hijira da kasar Kamaru ta tanada masu. To sai dai yanzu suna fuskantar barazanar karewar abinci da kuma rashin magunguna. Kawo yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya bata isa garesu ba.
Wani da aka zanta dashi daga Fatokol yace mutane fiye da 250 sun riga sun mutu sabili da rashin magani da isasshen abinci. A Fatokol kawai kusan mutane 15,000 suke wurin. Yanzu makonni biyu ke nan sa suka samu abinci. Akwai wasu 9,000 dake cikin tsaunuka.
Alhaji Muhammed Kanar na hukumar bada agajin gaggawa ta arewa maso gabas ya tabbatar da sanin halin da 'yan Najeriyan suke ciki. Yace ya kai maganarsu sama domin a yi wani abu. Kokarin da suka yi su shiga da abinci ya cutura. Yanzu suna shirin su je kasar ta Kamaru su sayi abincin can kana su dawo da 'yan gudun hijiran.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.