Inda yace an kama mutumin ne a jiya Alhamis a wata unguwa da ake kira Agenteuil da ke makwabtaka da birnin Paris ta arewa maso yamma. Amma yace har yanzu ba wata kwakkwarar hujjar da zata sa danganta harin na Paris da kuma wanda aka kai a Brussels shekaran jiya.
Ministan ya bayyana cewa kwararrun ‘yan sandan warware bam na cike a unguwar tare da gabatar da aikinsu bayan hana zirga-zirga a unguwar. Tun dai harin Paris ne kasar ta Faransawa ke ankare da duk wani kyas! da suka jib a su yarda da shi ba.
Ya rufe da cewa, an sami kama mutane 75 tare da yin hukuncin dauri akan fiye da guda 28 tun bayan kai harin na ranar 13 ga Nuwambar bara a Paris da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100 ya jikkata bila adaddin.