Najim Laachraoui, haifaffen kasar Morocco ne wanda ya girma a Brussels, hukumomi sun bayyana shi cikin mutanen da suka shirya harin Paris, bayan da aka gano sinadarin kwayar halittarsa jikin rigar da masu kunar bakin waken suka saka. Haka kuma an kara samun sinadarin halittarsa a gidan da jami’ai suka yi imanin an hada boma boman da aka yi amfani da su.
A jiya Laraba ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace, an gano dan kunar bakin wake na biyun, shine wanda a baya aka kama shi a Turkiyya kuma aka mayar da shi Turai aka kuma sake shi watanni 8 da suka gabata.
Erdogan yace gwamnatinsa ta gargadi hukumomin Brussels akan Ibrahim el-Bakraoui, wanda aka kama a kudancin Turkiyya a yayin da yake kokarin tsallakawa zuwa Siriya. Shugaban na Turkiyya yace tun watan Yulin shekarar da ta gabata aka tura shi Turai, amma duk da gargadin da aka yiwa hukumomin sai da suka sake shi.