Yansandan kasar Belgium sun gabatarda hoton wanda ake nema saboda kyautata zaton yana hannu a hare-haren ta'adanci da aka kai a filin saukan jiragen sama da kuma tashoshin jiragen kasa a Brussels babban birnin Belgium.
Hare-haren sun hallaka akalla mutane 30 tare da raunata wasu fiye da 230. Akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa.
Hoton da yansandan suka fitar ya nuna wani sanye da bakar hula da tabarau yana tura abun daukan kaya kamar yadda fasinjoji ke yi. Tare dashi akwai wasu maza biyu cikin bakaken kaya wadanda ake zaton su ne 'yan kunar bakin waken.
Hukumomin kasar ta Belgium sunce mutumin da suke nema ya arce amma suna cigaba da bincike. A binciken da suke yi 'yansanda sun gano wani bam da wasu sinadirai da suka hada da kusoshi da tutar kungiyar ISIS.
Kawo yanzu dai ita kungiyar ISIS ta riga ta dauki alhakin kai hare-haren jiya Talata