Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na ganawa yau Alhamis da takwaransa na kasar Rasha, Sergei Lavrov da kuma shugaba Vladimir Putin don tattaunawa akan rikicin Siriya da Ukraine.
Kerry ya fada kafin tattaunawarsa da Lavrov, cewa mutane da yawa na fatan wannan tattaunawar da ake yi a Moscow za ta taimaka wajen gaggauta kawo karshen rikicin Siriya. Ya kuma kara da cewa ya na fatan samun hadin kai daga Rasha wajen fuskantar rikicin Yemen, da Libiya, da kuma shirin samar da zaman lafiya da ake yi a gabas ta tsakiya.
Kerry kuma ya ce yarjejeniyar Siriya ta kawo dan cigaba, yana mai cewa, ta na da rauni amma duk da haka an sami raguwar tashe-tashen hankula.
Ana sa ran Kerry zai nemi amsoshi daga Rasha akan matsayarta dangane da kafa gwamnatin rukon kwarya a Siriya.
A ganawarsa da Lavrov, ta yiwu Kerry ya tattauana akan hare-haren da aka kai a birnin Brussels. Sakatare Kerry ya ce wadannan hare-haren an yi su ne ga al’ummar Belgium da ma Turai.