Kasar Turkiya ta bada sanarwa cafke wasu mutane guda bakwai a wasu sassan birnn Istanbul.
Hukumomin kasar sun zargi mutanen da kasancewa 'yan kungiyar ISIS ne dake kokarin shiga kasar domin aikata ta'adanci.
'Yansandan kasar sun samu nasarar cafke mutanan ne sanadiyar wan samamae da suka kai jiya Talata a wurare da dama a babban birnin kasar Istanbul biyo bayan harin da aka kai can baya da kungiyar ISIS ta dauki alhaki.
Bayyanan leken asirin siri da 'yansandan kasar Jamus suka tattara ya sa 'yansandan Turkiya suka kai samamen domin gudun kada a sake kai hari a kasar kamar yadda aka kai kan wasu muradun kasar Jamus da suke Istanbul.
Haka ma jiya Talata jami'an tsaron kasar sun hana wasu su goma da ake zaton 'yan kungiyar ISIS ne tsallakowa daga Syria zuwa cikinkasar. Jami'an Turkiya na zaton mutanen suna kokarin shirin ta'adanci ne saboda daya daga cikin mutanen yana sanye da rigar kunar bakin wake da yake shirin tarwatsawa