Lura da yadda akasarin jama’a ke nuna halin ko in kula da ka’idodin kariya daga kamuwa da cutar coronavirus duk kuwa da cewa alamu na nuni da tun daga farkon watan Nuwamba zuwa yau cutar ta yadu a dukkan sassan kasar Nijer a zagaye na biyu, lamarin da ya sa shugabanin kwamitin yaki da wannan annobar sake nanata kira ga al’uma game kare kai daga cutar kamar yadda ministan kiwon lafiyar al’uma Ahmed Boto ya yi bayani a taron manema labaran da aka kira a jiya Talata.
Ya ce al’umma bata bin ka’idojin da hukumomi suka gindaya, shi ya sa cutar ta bazu a ko ina. A cewar sa gwamnatin na iya bakin kokarinta kuma tana kashe makudan kudade wurin yaki da wannan cuta, dan haka dole ne mutane su baiwa gwamnati hadin kai domin cimma wannan yaki.
Boto ya bayyana cewa gwamnati Nijer na shirin gudanar da aikin bada allurar rigakafi a kasar kamar yadda aka fara a wasu kasashen duniya, yana mai cewa nan da watanni uku masu zuwa za a fara bada allurar, dan haka gwamnati na bukatar goyon bayan al’umma domin samun nasarar aikin bada rigakafin.
A jajibirin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da suka gudana a ranar 27 ga watan Disamban da muke ciki masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa hukumomin Nijer na faman fakewa da anobar COVID-19 don hanawa jama’ar kasar sakewa gabanin fitar da sakamakon zabe a bisa zargin yiwuwar tafka magudi, zarin da ministan kiwon lafiya ya ce babu kamshin gaskiya a wannan zarge.
Ministan ya ce ma’aikatar kiwon lafiya bata saka siyasa a cikin aikinta, babbar manufarta ce ta kare lafiyar al’ummar kasa kana ta yi kira ga al’umma ta bi sharudan kare kai daga annoba. Sai dai ya kara da cewa idan akwai bukatar daukar matakai lallai gwamnatin zata dauki matakan da suka dace tare da tsaron al’umma amma ba dan biyan bukatun siyasa ba.
A makon jiya gwamnatin Nijer ta bada sanarwar rufe gidajen shan barasa da wuraren shakatawa hade da illahirin makarantun bokon kasar sandiyar wannan cuta yayinda aka gargadi faisinjoji su saka takunkumi a motocin jigila sai kasuwani da tashoshin shiga mota.
Shugabanain kwamitin yaki da cutar covid 19 a taron ‘yan jaridar na yau talata sun sanar cewa mahukunta sun kudiri aniyar soma hukunta dukkan wadanda ke bijirewa matakan riga kafin dakile wannan masifa.
Ga dai rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai: