Kungiyar kasashen da ke yankin Sahel CEN-SAD, ta nuna gamsuwarta dangane da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar cikin lumana, tana mai kira ga al’umar kasar da su nuna goyon bayan ga shugaban da ya samu nasarar wannan zabe.
Kungiyar ta yi kira ga jam'iyun siyasa da sauran daidaikun al'umma cewa, duk wanda ke da korafi kan zaben, ya bi hanyar da doka ta tanada domin a bi masa kadinsa.
A cikin hirar shi da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma,daya daga cikin jagororin kungiyar Sanata Lawal Gana Guba, ya yi bayani kan yadda kungiyar ta CEN-SAD ta kalli zaben.
Sanata ya ce, sun shaida kayan zabe sun isa akan kari, sun shaida akan samar da jami'an tsaro a duk runfunan zabe, sun kuma shaida cewar mutanen kasar sun yi gagarumin fita runfunan zabe kdon kada kuri'unsu.
Ya bayyana gamsuwa tare da cewa. zaben ya bada mamaki ga duk wanda ya gani, domin kuwa ba a shiga hakkin 'yan kasa ba, babu wata takura, an kuma gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kungiyar ta bada shawara ga duk 'yan takara akan sakamakon zabe. Sanata Lawal Gana Guba ya ce, "Abu na farko sai anyi hakuri, kana abu da kawai ake bukatar duk wanda yake da ja akan sakamakon zaben, to ya garzaya kotu, domin kuwa akwai dokoki da suka tanaji yadda mutane zasu kalubalanci zabe, babu bukatar a tada hankali."
Saurarri cikakken tattaunawar a cikin sauti.