Zaben na zuwa ne bayan na gama-gari da aka gudanar a jiya Lahadi 27 ga watan nan, ya na kuma wakana ne saboda kayan aikin zabe da ba su isa yankin akan kari ba a cewar hukumar ta CENI.
“Jiya da karfe bakwai na yamma kayan aiki suka isa, saboda lamarin matsalar tsaro a yankin, dalili kenan da ya sa jami’an tsaro suka ce a bari sai yau Litinin a yi zaben.” abinda Nafi’u Wada, kakakin hukumar CENI ya fadawa manema labarai kenan.
A cewar Wada, rumfunan zabe biyu ne a yankin kuma tun da misalin karfe shida na safe aka bude su, “saboda rana ta na saurin fitowa fiye da birnin Yamai.”
Madama, yanki ne mai Hamadar Sahara da ya hada iyaka da kasar Libya wacce ke fama da rikice-rikicen siyasa.
A jiya Lahadi ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a daukacin kasar ta Nijar inda ake dakon sakamakon zabe.
‘Yan takara 30 ne ke neman kujerar shugaban kasa ciki har da tsohon ministan cikin gida Mohamed Bazoum da ke takara a karkashin jam’iyyar PNDS mai mulki.
Sai kuma Mahamane Ousman na jam’iyyar RPR wanda ake ganin da shi za su fafata da Bazoum la’akkari da cewa babbar jam’iyyar adawa ta Moden Lumana ta mara mai baya.
Kujerun majalisar dokoki 171 ake takara akansu a wannan zabe.