Bisa doka, hukumar zabe ta CENI na da kwana biyar kafin ta kammala kidayar ta kuma fitar da sakamakon zaben. Ana dai tsanmanin sakamakon zaben nan da ‘yan kwanaki.
Mika Mulki daga wata gwamnatin zuwa wata abu ne mai muya, musamman ga kasar da ta fuskanci juyin Mulki na soji har sau 4, tun bayan samun ‘yancin kanta daga turawan Faransa a shekarar 1960, kasar kuma tana fama da talauci, da ‘yan ta’adda masu tada kayar baya, wadanda suka kashe daruruwan fararen hula, tare da sojoji a cikin shekarar da ta gabata kawai.
Haka kuma za a samu banbanci kamar irin yadda aka samu a Ivory Coast da Guinea, inda shugabanin kasar a cikin wannan shekarar suka sauya kudin tsarin mulkin kasar don su kara wa’adin mulkinsu zuwa zango uku uku. Wannan ya haifar da fargaban yiwuwar samun koma bayan damokaradiya a kasashen yankin hamada.