Hukumar zabe ta Najeriya, ta gudanar da wasu canje-canje da ya shafi karban katunan ragistan masu zabe a ciki kasar.
Huklumar ta dage shirye-shiryen da tayi ada daga watan nan na yuli zuwa watan Augusta wanda ake sa ran ‘yan kasa daban-daban daga jihohi guda goma na farko zasu fara karkan katunansu na zabe na dindindin a cikin Najeriya.
Daya daga cikin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa Amina Zakari, tace hukumar ta rega tayi kashin na farko a watan da ya wuce, yanzu kuma wanda da za’a yi a cikin wannan watan an daga shi zuwa watan Augusta.
Ta kara da cewa jihohin da za’a yi goma ne Sokoto, Jigawa, Oyo, Ondo, Ebonyi da Anambra. Sauran sun hada da Babban birnin taraiya Abuja, Kwara, Yobe da Bauchi. Tace kowane yanki nada jihohi biyu.
Yanzu dai ‘yan kasa sun tukufa domin yin amfani da wannan lokaci sabo da hukumar zabe ta fitar domin wadanda basu da katunan zabe ko kuma suke da matsaloli da katunan su a yanzu su tabbatar ganin cewa sunyi amfani da wannan damar domin warware matsalar.
Domin ta hanyar gada kuri’a ne kawai ‘yan kasa zasu iya damar da suke da ita na canja ko kuma tabbatar da shuwagabaninsu dake mulki a yanzu.