Duk da hutun dole na kwanaki biyu da Gwamnatin jihar Adamawa ta bada yanzu haka kwamitin da mataimakin Cif jojin Adamawa mai sharia Ambrose Mamadi, ya kafa sun fara zama don jin ba’asi game da tuhumar da ake yiwa gwamna Murtala Nyako da mataimakinsa Bala James Ngalari.
Tun farko babban magatakardan kotunan jihar Adamawa, Alhaji Abubakar Bayola, ya bayanawa manema labarai cewa abisa doka ba dole ne sai mataimakin Cif jojin ya rantsar da ‘yan kwamitin ba, batun da wani masanin harkar sharia Barister Sunday Joshua yayi Karin haske akai.
Yace “ a bisa doka abu mafi mahimmanci shine kafa kwamitin baiwa rantsar da kwamitin ba, yanda aka kafa kwamitin an kafa a bisa doka rantsar da kwamiti harka ce na biki ba lalle bane sai anyi ba, domin abisa doka idan aka kafa kwamiti daga ranar da aka kafa suna da kwanaki chasa’in su gama bincike akan zargin da akeyiwa Gwamna.”
Wasu magoya bayan Gwamnan jihar, kamar Ibrahim Baffa Waziri, yace “ alama ya nuna cewa demkradiyar Najeriya, yaso karshe idan har shuwagabanin kasa zasu zauna suyi wannan abun, ance an nada kwamiti mun yarda an nada kwamiti, muna jira muga abunda mataimakin babban mai sharia zai yi, sai muka ji cewa ‘yan kwamiti zasu rantsar da kansu, na farko sun saba doka na biyu da mun dauka dattawa ne ‘yan kasa masu kishin kasa gashi mun fahimci cewa kishin da sukeyi kishin kudin da za’a basu ne. = Gashi kuma mun sansu mun san ‘yayansu mun san iyalansu, abun zai kasance abun takaici abun kunya abun Allah wadai.”
Sai dai yayin da wasu ke suka ga ‘yan siyasa, Francis Hamani na ganin matakin da ‘yan majalisar suka dauka yayi daidai idan yace “ ana take hakin mutane, dole ne idan an take hakin ‘yan mutane ‘yan majalisar masu wakiltan mutane sunyi aikin da yakamata.