An kira gwamnatocin jihohi, kungiyoyi, da masu hannu da shuni da su tallafawa gwamnatin tarayya wurin inganta ilimin jami'o'i a Najeriya.
A wata gidauniya da jami'ar Jos ta kafa domin inganta ilimin dalibai ta hanyar samarda dakunan karatu, naurorin gwaje-gwaje da bunkasa kwasakwasai a jami'ar aka yi kiran.
Dr Muhammed Bashar Nuhu kwamishanan ilimi mai zurfi na jihar Neja wanda kuma ya wakilci gwamnan jihar Dr Babangida Muazu Aliyu yace batun ilimi haki ne na kowa da kowa. Sabili da yawan jama'a a kasar dole ne sai an bayar da gudunmawa. A manya manyan makarantu na duniya gwamnati bata da hannu a cikinsu. Dalibai da aka yaye da kamfanoni da masu hannu da shuni su ne suke taimakawa. A Najeriya kadai da kasashe masu tasowa ake ganin gwamnati tana bada kudade.
A jihar Neja yace sun yi nisa da batun ilimi. Duk wanda zai bude jami'a zasu bashi fili su kuma biya kudin diyan filin.
Farfasa Onje Gewado ya tabo wasu matsaloli da jami'o'i ke fuskanta a kasar. Akwai karancin azuzuwa da kayan aiki da malamai. Ingancin daliban da ake yayewa yanzu ya ragu.
Shugaban jami'ar Farfasa Babale Mafuyai ya bayyana takaicinsa na ganin cewa kusan shekaru arba'in da bude jami'ar har yanzu wasu sassa nata na harabar wucin gadi duk da cewa jami'ar na ba dalibai kusan dubu biyar gurbin karatu a kowace shekara. An kafa gidauniyar ne domin a bunkasa kwasakwasan jami'ar tare da kafa wasu sabbi kamar na sashen noma da injiniya da kiwon lafiyan dabbobi. Gwamnati ba zata iya yi masu duk abubuwan da suke so ba dalili ke nan suke neman taimako.
Ga karin bayani daga Zainab Babaji.