Lauyoyin gwamna Murtala Nyako sun mayar da martani game da cigaba da yunkurin tsige gwamnan jihar Adamawa da mataimakinsa Bala John Ngilari da 'yan majalisar keyi.
Yan majalisar sun sa hannu a wata takardar da suka mikawa alkalin alkalan jihar inda suka bukaceshi da ya kafa kwamitin bincikar gwamnan cikin gaggawa lamarin da lauyoyin suka ce keta dokokin shari'a ne. Sun zargi majalisar da keta doka.
Barrister Ayo Akanmu yace abun da 'yan majalisar suka yi sun raina kotun ne domin akwai wani umurnin dakatarwa da kotun ta bada tun farko kuma jiya Laraba ne umurnin zai kare. Yace matakin da suka dauka ba bisa doka yake ba sabili da haka zasu kalubaleshi a gaban shari'a.
Masanin harkokin majalisa Ibrahim Baffa Waziri tsohon dan majalisar dokokin jihar yace abun dake faruwa alama ce dimokradiya ta dauki hanyar mutuwa domin babu yadda za'a ce magana na gaban alkali kuma yace su dakata har sai ya bayar da hukunci yau ko gobe kana su 'yan majalisa su yi gaban kansu. Alkalin alkalan jihar shi ya bada umurnin kuma yanzu shi suka ba takardar ya nada wadanda zasu binciki gwamnan. Shin ta yaya alkalin alkalan zai nada kwamitin binciken gwamnan bayan umurnin da ya riga ya bayar. 'Yan majalisar sun yi garaje. Yau ya kamata su zauna su dauki shawararsu.
Tuni 'yan siyasa suka soma mayar da martani dangane da matakin da 'yan majalisar suka dauka. Dr Umar Duhu daya daga cikin shugabannin siyasa a jihar yace abun dake faruwa 'yan majalisar basu nemi shawarar mazabunsu ba. Hankalin mazabunsu ya tashi domin tamkar basa jin kira ne. 'Yan majalisa basu nuna dattaku ba. Sabili da haka suna neman hanya a siyasance su shawo kan lamarin.
Amma kakakin majalisar Ahmed Umaru Sintiri yace su da kyakyawar niya suke aiwatar da kudurinsu. Yace sun dauki matakan ne domin an dagula harkokin aikin gwamnati a jihar babu cigaba. Mutane suna cikin kuncin wahala. Haki ne akansu idan an kai irin wannan halin da ake ciki su tashi su ceto al'ummarsu. Matakin da suka dauka na ceto ne.