Yayin da majalisar dattawan Najeriya ke sukar lamirin gwamnatin Imo na yiwa 'yan asalin arewa ragista kafin su cigaba da zama a jihar, wasu mazauna jihar sun bayyana ra'ayoyinsu.
Faisal Lawal mai ba gwamnan jihar Imo shawara akan baki dake zaune a jihar yace zama aka yi sabili da halin da ake ciki. A yankin kudu maso gabas duk lokacin da aka ga mutum da dogayen kaya sanye, sai a soma zarginsa da cewa watakila dan ta'ada ne. Amma duk wanda yake da takardar shaidar irin aikin da mutum yake yi babu mai zarginsa.
Alhaji Baba Saidu Suleiman sarkin hausawan jihar Imo yace yana zaune aka kawo kati akan cewa ya sa hannu domin duk mazaunin jihar da ya kasance dan arewa yakamata yana da katin shaidar cewa mazaunin gari ne. Gwamnatin na son tantance 'yan arewa dake jihar sabili da rikice-rikice dake faruwa.
Wadanda lamarin ya shafa kai tsaye sun bayyana ra'ayoyinsu. Alhaji Hamza Abdullahi Marafan Imo yace su basu san ma'anar katin ba. Yace idan an ce sai sun yi kati za'a gani kamar su 'yan arewan ne ke cuta. Shi Alhaji Abdullahi Dikko yace a yi katin domin zai ban-banta mutanen kwarai daga muggaye. Alhaji Shehu Kwanti yace su basu yadda da maganar yin kati ba.
Kwamishanan rundunar 'yansandan jihar Imo Abdulmajeed Ali yace shiri ne da gwamnan Imo ya fito dashi kuma shiri ne na samun zaman lafiya. Yace jihar Enugu ta fara kafin jihar Imo.
Barrister Muhammed Ahmed Jamo yace sashi na arba'in a kundun tsarin mulkin kasar ya haramta kafa dokar da zata nuna banbanci ko na addini, kabilanci ko asalin mutum a koina. Kudurin gwamnatin Imo ya sabawa tanadin kudun tsarin mulkin Najeriya.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.