Ayyana yau da gobe a matsayin ranakun hutu da gwamnatin jihar Adamawa tayi tamkar hana kaddamar da kwamitin da zai binciki gwamnan ne wanda mukaddashin alkalin alkalan jihar ya kafa.
Ta bakin kakakin gwamnatin jihar Ahmed Sajoh yace an dauki matakin bada hutun ne domin a aiwatar da addu'o'i na musamman dangane da abubuwan dake faruwa a jihar da ma Najeriya gaba daya.Yace suna son mutane su yi nazari su yiwa Allah godiya kana su roki Allah Ya kawo zaman lafiya.
To amma tuni wannan matsayin da gwamnatin jihar ta dauka ya jawo cecekuce. Sakataren PDP Barrister A.T. Shehu yace bada hutun shure-shure ne wanda ba zai hana mutuwa ba. Koda hutun wata daya gwamna ya bayar ba zai shafi abun da mukaddashin alkalin alkalan jihar ya riga ya kaddamar ba. Gwamnan na ganin idan ba'a kaddamar da kwamitin da aka kafa ba babu abun da za'a yi domin wa'adin alkalin alkalan zai kare nan da kwana biyu. To amma bakin alkalami ya riga ya bushewa gwamnan saboda kundun tsari bai ce a kaddamar da kwamiti ba kafin yayi aikinsa.
Saidai jam'iyyar APC tace hutun da gwamnan ya bayar yayi daidai. Duk lokacin da gwamnati ta bada hutu duk aikin da aka yi a cikin lokacin baya bisa doka.
Ga karin bayani.