Da yake magana a taron manema a Hedkwatar hukumar tsaron Farin Kaya ta SSS dake babban birnin Abuja, Kakakin hukumar Mallam Abdullahi Garba, yace ba gaskiya bane abinda ake ta fada na cewa ‘dan majalisar Dokokin jihar Ekitin nan da take tsare da shi bisa ga laifin da ya shafi barazana ga tsaron kasa Hon Afolabi Akanni ya mutu a hannun ta.
Kakakin na hukumar ta SSS na Najeriya, Mallam Abdullahi, yace kudai ga Mr. Afolabi cikin koshin lafiya da nutsuwa, duk kuwa da yadda ya kanannade ya langwame ya lanjane yaki magana da ku yan jaridu.
A gefe guda kuma majalisar dokokin jihar Ekiti na birnin Abuja, inda ta maka hukumar SSS gaban hukumar kare yancin bil Adama ta Najeriya. jagoran ‘yan majalisar Samuel Omotosho, yace ranar hudu ga watan Maris, jami’an hukumar SSS na Najeriya, sun afkawa majalisar dokokin jihar Ekiti daga bisani kuma wakilan guda hudu sukayi batan dabo, sai bayan kwanaki hudu hukumar SSS din suka ce Hon Afolabi Akanni yana hannunsu.
Haka kuma sunce ba a bar kowa ya ganshi ba, koda lauyoyinsa masu kare shi basu sami ganin sa ba. ‘yan majalisun sunce sun samo hukuncin wata babbar kotu na a sake shi amma SSS taki bin umarnin kotun.
Sai dai kuma hukumar SSS tace babu wani umarnin kotu da ta samu akan wannan magana, inji kakakin hukumar ta SSS Mallam Abdullahi Garba.