Ministan Alhaji Ibrahim Jibrin ya halarci taron shekara shekara da Bankin Duniya ke shiryawa akan abun da ya jibanci matsalolin dake addabar mutanen duniya musamman akan muhalli.
Babban Bankin Duniya na yin bincike akan matsalar filaye musamman matsalar handame filaye da attajirai ke yi lamarin da kan shafi talakawa su rasa wurin dafawa ko cigaba da rayuwarsu.
Bankin duniya yana taimakawa kasashe su shawo kan irin wadannan matsalolin a kasashe masu tasowa kamar su Najeriya da Ghana.
Wata matsala da ta shafi Najeriya ita ce sare itatuwa da gina hanyoyi dake tsarawa cikin dazuka da gwamnati ke karewa. Idan aka shiga sare itatuwa a dazuka yana harzuka dumamar yanayi musamman a yankin arewacin Najeriya.
Domin shawo kan irin wannan matsalar an kafa wata hukuma da zata dinga shuka itatuwa a wasu jihohin Najeriya kama daga kudancin kasar har zuwa arewanci. Ya zama wajibi a kare muhalli domin kowace shekara hamada na kara shigowa.
Gwamnatin Najeriya tana neman hanyar rage sare itatuwan da ake makamashi dasu. Hanyar rage illar itace idan an sare itace daya a shuka biyu. Hanya ta biyu ita ce samar masu da sabon makamashi da mutane zasu yi anfani dashi. A yi anfani da iskar gas ta yadda mutane zasu iya yin anfani dashi
Ga karin bayani.