A cikin kasafin kudin bana na kasar Najeriya majalisan dattawan kasar ta ware nera biliyan goma domin gwamnati ta taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabas musamman a jihohin Adamawa, Borno da Adamawa.
Majalisar tana son gwamnati ta gaggauta mayar da wadanda suke gudun hijira sanadiyar rasa muhallansu, makarantu, asibitoci, da sauran wuraren jin dadin jama'a gabanin kafa gidauniyar farfado da yankunan nan gaba.
To saidai al'ummomin da lamarin ya shafa sun soma kira da a sa ido game da yadda za'a kashe kudaden.
Suna cewa sun ji an ware kudi dominsu. A tasu ra'ayin duk wadanda aka yi masu barna sai a raba masu kudin kowa ya kama gaban kansa. Mai son gyara ya yi wanda kuma zai yi jari da kudin ya yi. Suna tsoron wasu zasu saka kudin cikin aljihunsu su kuma a barsu da hamma.
Yayinda ake shirin mayar da 'yan gudun hijiran zuwa garuruwansu wasu cikinsu na cewa a tabbatar an kwato duk wuraren daga hannun 'yan Boko Haram domin har yanzu akwa zaman dar dar a wasu wuraren.
Yanzu dai jihar Adamawa na shirin karbar 'yan gudun hijira su dubu hamsin da shida daga kasar Kamaru. Gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindo Umaru Jibrilla yace yana neman taimakon gwamnatin tarayya da bankin duniya.
Ga karin bayani.