A wata hira da kamfaninnin dillancin labarai na Najeriya, mai ba kasar China shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a ofishin jakadancin China dake Najeriya, Zao LingXiang, yace, a ra’ayinsa, ba abin damuwa bane ko Iran ta sake shigowa ko babu. Kamfanonin China suna so su kara yawan danyen Mai da suke saya daga Najeriya.
Kimanin ganga miliyan daya ne kasar China ta saya daga Najeriya bara, kwatankwashin kashi daya da digo uku cikin dari, na danyen Man da Najeriya ta sayar a kasashen duniya. LinXiang yace cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai na dala biliyan 15, ya zama Najeriya ta kasance ta uku a jerin kasashen da China ke huldar cinikayya dasu a nahiyar Afrika.
China ce babban abokiyar cinikayyar kasashen Afrika. Banda danyen Mai, kayan da China ke huldar cinikayya da Najeriya sun hada da injuna, da kayan ayyukan sufuri, tufafi, kayan daki, magunguna da kuma na’urar Komputa.
Wannan ci gaban yana da muhimmanci ga Najeriya kasancewa arzikin kasar ya dogara kan albarkatun Mai, inda gwamnati ke samun kashi tamanin cikin dari na kudin shigarta daga albarkatun Mai. Najeriya ta sami koma bayan tattalin arziki sakamakon faduwar farashin Mai tun daga watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.
Buhari da gwamnatin Najeriya suna daukar matakan neman wadansu hanyoyin samun kudaden shiga, bisa ga tsarin kungiyar hadin kan kasashen Afrika goma da China, da aka sanar a wani taron koli da aka gudanar a birnin Johannesburg bara, kan harkokin cinikayya da China.