An tsare Hama Amadou a gidan yari tun watan Nuwamba bisa zargin safarar jarirai, zargin da shi da magoya bayansa suce ce bita da kullin siyasa ne.
Jami’an hamayya sunce Amadou ya jima yana fama da rashin lafiya tunda aka daure shi, sai dai ba a san ainihin abinda ke damunsa ba.
Hama Ahmadou tsohon kakakin majalisa , yana so a sa sunansa a katunan zaben da za a gudanar ranar Lahadi ko da yake makon jiya, gamayyar kungiyoyin hamayya da yake jagoranta suka yi barazanar kauracewa zaben
Suna zargin cewa, sakamakon zaben da shugaban kasa mai ci yanzu Mahamadou Issoufou ya lashe na boge ne.
Gamayyar jam’iyun hamayyar sun kuma zargin kotun kolin kasar da hada baki da gwamnati da nufin ganin an sake zaben shugaba Mahamadou Issoufou. Suna zargin shugaban kasar da mulkin kama karya.
Duk da albarkatun makamashi da Nijar ke da shi, tana daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya.