Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Henry Okah Yana Bayyana Gaban Kotu Yau A Afirka Ta Kudu


Henry Okah Yana Bayyana Gaban Kotu Yau A Afirka Ta Kudu
Henry Okah Yana Bayyana Gaban Kotu Yau A Afirka Ta Kudu

Tsohon madugun na Kungiyar MEND zai fuskanci tuhume-tuhume masu alaka da hare-haren bam da suka kashe mutane akalla 12 cikin wannan wata a Najeriya

Wani tsohon madugun tsagera a Najeriya zai bayyana gaban kotu yau alhamis a kasar Afirka ta Kudu domin fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da hare-haren bam da suka kashe mutane akalla 12 cikin wannan wata a Najeriya.

Ana tuhumar Henry Okah, wani tsohon madugun kungiyar tsageran yankin Niger Delta ta MEND da laifin gudanar da ayyukan ta’addanci da kuma hada baki domin kai tagwayen hare-hare cikin mota a Abuja, ranar bukukuwan cikar shekaru hamsin da samun ‘yancin kan Najeriya.

Okah yana tsare a gidan kurkuku a Afirka ta Kudu tun lokacin da aka kama shi a farkon wata. Hukumomin Najeriya sun kama wasu mutanen 9 dangane da hare-haren. A makon da ya shige wasu shugabannin kungiyar MEND sun ce ba su ne suka kai harin ba, duk da takardun sanarwar daukar alhakin hare-haren da wannan kungiya ta bayar a can baya.

XS
SM
MD
LG