: Yan sanda sun bayyana sunayen mutane biyu, yan nijeriya, da ake zargi da jagorantar tayar da bama-baman ranar Jumma’a wajen bikin zagayowar ranar samin yancin kan Nijeriya, wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane 12.
Jiya Lahadi yan sanda sun ce wadanda ake zargin su ne Ben Jessy da Chima Orlu kuma sun bayyana hotunansu amman ba su yi wani karin bayani ba.
Mayakan sa kai a Nijeriya da ake kira kungiyar MEND sun yi ikirarin kai harin na ranar Jumma’a. Kungiyar ta MEND ta yi ta kai hare-hare da garguwa da mutane sau da dama a Nijeriya.
Kungiyar ta ce ta na son a dada yin mata adalci wajen yawan kason da ake ware mata daga dukiyar arzikin man fetur na kasar kuma sun fi auna kamfanonin man kasashen waje.
To amman tsohon shugaban MEND Henry Okah, wanda aka damke shi a Afirka ta Kudu ranar Asabar, ya wanke kansa daga hare-haren na ranar Jumma’a.
Haka zalika, Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya nuna shakku game da ikararin da kungiyar MEND ta yi na kai harin.
A wani bayanin da ya yi jiya Lahadi, ya zargi wata yar karamar kungiyar ta’addanci daga kasar ketare da kai hare-haren, to amman bai yi wani karin bayani ba.