Jami'ai a Najeriya sun ce mutumin da suke kyautata zaton shi ya kulla harin bam da aka kai a Abuja, babban birnin kasar, a ranar 1 ga watan Oktoba, shi ne kuma ya kulla harin bam da aka kai a farkon shekarar nan a yankin kudancin kasar mai arzikin man fetur.
Wata mai magana da yawun hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya, SSS, Marilyn Ogar, ta ce Henry Okah ya taimaka wajen shirya harin bam da aka kai cikin watan Maris a birnin Warri inda ake hada-hadar man fetur a kudancin Najeriya.
An yi imanin cewa Okah shi ne tsohon madugun babbar kungiyar 'yan tsageran yankin Niger Delta, watau MEND.
A yanzu haka yana fuskantar tuhume-tuhumen aikata ta'addanci a kasar Afirka ta Kudu, inda yake zaune, a saboda zargin cewa yana da hannu a tagwayen hare-haren bam na mota da suka kashe mutane 12 a ranar 1 ga watan Oktoba a Abuja. Okah ya musanta cewa da hannunsa a harin.
Jiya laraba, jami'an Najeriya sun yi zargin cewa Okah ya tafi Najeriya a jirgin sama daga Afirka ta Kudu a watan Maris, domin shirya harin bam din da aka kai cikin mota a Warri.
Suka ce wannan bam ya tashi a kofar wani ginin gwamnati a lokacin da ake tattaunawa a kan shirin ahuwar da gwamnati ta yi wa tsagera na yankin Niger Delta.