Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace 'yan ta'adda ne suka kai harin da tagwayen boma bomai da ya kashe mutane goma sha biyu,ranar Jumma'a,kusa da inda aka yi bukukuwan ranar samun 'yancin kai a Abuja.
Mr. Jonathan yace wadanda suka kulla makarkashiyar kai harin sun fake ne da matsalolin da ake fuskanta a yankin Niger Delta domin cimma burinsu.
Babbar kungiyar fafutuka a yankin Niger Delta, ko MEND a takaice ta dauki alhakin kai harin,wanda kuma ya jikkata wasu mutane 17. MEND tace an yau shekaru hamsin kenan aka sace kasarsu da albarkatunta.
Cikin sanarwa da ta bayar ranar jumma'a, kungiyar MEND ta gargadi jami'ai gameda harin boma boman,sa'o'i gabannin ya faru. Jaridun Najeriya sun bada labarin cewa,hukumar leken asiri ta Ingila ta sami labarin harin,kuma ta sanarwa gwamnatin Najeriya.Jaridar This Day tace,jami'an tsaron Najeriya suka kasa tarwatsa yunkurin. Jami'ai suka ce saboda samun labarin harin tun farko,mutuminda zai wakilci sarauniya Elizabeth a bikin ya fasa zuwa.Haka shima tsohon PM Ingila Gordon Brown,wanda da ya shirya halartar bikin bai je ba.