An tsare wani dan Najeriya a Afrika ta Kudu dangane da tagwayen hare haren boma bamai da aka kai ranar jumma’a da suka yi sanadin mutuwar mutane goma sha biyu, kusa da inda ake bukukuwan samun ‘yancin kai, a babban birnin tarayyar kasar. Kakakin rundunar ‘yan sandan ciki ta Najeriya Marilyn Ogar, ta shaidawa manema labarai jiya asabar cewa, ‘yan sanda a Johannesburg, Afrika ta Kudu, suna tsare da wani mutum da ake kira Henry Okah. Okah shine tsohon shugaban kungiyar Movement for the Emancipation of Niger Delta, ko MEND, wadda ta dauki alhakin fashe-fashen. Kungiyar mayakan ta ce an shafe shekaru hamsin ana sacewa mutanen Niger Delta kasa da kuma albarkatunsu. Kungiyar MEND ta yi gargadi dangane da fashe fashen sa’a daya kafin suka auku ranar jumma’a. Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace wadanda suka kai harin, suna fakewa ne da fafatukar yankin Niger Delta mai arzikin man fetir domin cimma wata manufa ta kashin kansu.