Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tafi Najeriya


Wasu daga cikin makaman da aka kama cikin kwantena a Lagos
Wasu daga cikin makaman da aka kama cikin kwantena a Lagos

Jami'an Najeriya sun ce Manouchehr Mottaki ya je shi ne domin tattaunawa kan makaman da aka kama kwanakin baya, wanda kuma ake zargin ya fito ne daga Iran

Jami'an gwamnatin Najeriya sun ce ministan harkokin wajen Iran ya je shi Najeriya domin tattaunawa a bayan da aka gano wasu makaman da aka yi zargin cewa sun fito ne daga kasar Iran.

Jami'an Najeriya sun tabbatar da cewa Manouchehr Mottaki ya gana da takwaran aikinsa na Najeriya, Odein Ajumogobia, alhamis a birnin Lagos.

Mr. Ajumogobia ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne a kan wadannan makamai da aka samu cikin kwantena. Ya ce ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatarwa Najeriya cewa gwamnatin Iran zata bayar da hadin kai ga binciken da ake gudanarwa game da wadannan makamai.

Makonni biyu da suka shige ne hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya ta kama kwantean dake dauke da wadannan makamai wadanda suka hada da rokoki, da harsasan manyan bindigogi, da gurneti da wasu nakiyoyin.

Wani kamfanin safarar jiragen ruwan kasar Faransa mai suna CNA-CGM, wanda ya kai kwantena dake dauke da makaman zuwa Najeriya, ya ce an yi masa lodinsu ne a kasar Iran. Kamfanin yace takardun da aka manna a jikin akwatunan dake dauke da makaman sun nuna cewa duwatsu da gilashi ne a ciki.

Jami'an gamnatin Isra'ila sun ce an yi niyyar kai makaman ne zuwa Zirin Gaza dake hannun Hamas. Wani shugaban 'yan Hamas a gaza ya musanta cewa an yi niyyar kai musu wadannan makamai ne.

Najeriya tana zaman shirin ko-ta-kwana tun wani harin bam da aka kai lokacin bukukuwan samun 'yancin kai ranar 1 ga watan Oktoba a Abuja, har aka kashe mutane 12.

Wata kungiyar tsagera ta yankin Niger Delta, MEND, ta dauki alhakin kai harin.

XS
SM
MD
LG