Kantoman lardin Himatyat Ullah ya bayyana wa manema labarai cewa wani mahari da makami ne ya jefa gurneti akan masu tsaron kofar kotun kafin ya ta da bam da ke jikinsa.
Hukumomin da wasu majiyoyin asibiti sun ce akwai lauyoyi cikin wadanda wannan harin ya rutsa da su kuma akwai alamar yawan mutanen da suka mutu zai karu.
Harin bam din ya faru ne jim kadan bayan da sojojin Pakisatn su ka kashe wasu maharan kunar bakin wake su hudu kafin su ta da bam, a wata unguwar Krista da ke babban birnin Lardin na Pashawar.
Wata sanarwa da ma'aikatar sojin kasar ta fitar, ta ce maharan sun raunata sojoji biyu da dan sanda guda da kuma wasu fararen hula biyu.
Kakakin wani bangaren da ya balle daga kungiyar Taliban na Pakistan wato Jama'atul Ahrar (JuA) ya shaidawa VOA cewa kungiyar ce ke da alhakin wadannan hare hare biyu, koda yake ba za a iya gaggauta tabbatar da wannan abin da su ke fadi ba.