Kungiyar IS ta sanar da mutuwar Abu Muhammad al-Adnani jiya Talata, lokacin yana sa ido kan ayyukan kungiyar na shawo kan hare haren sojin da ake kaiwa a Aleppo.
Wani babban jami’in tsaron Amurka yace dakarun hadin guiwa sun kai farmaki jiya talata da safe da jiragen sama a al Bab na kasar Syria kan shugaban kungiyar. Bai fadi ko an kai harin kan Adnani bane ko kuma an kashe shi. Yace jami’an Amurka suna kan nazarin sakamakon farmakin.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tayi tayin bada tukuicin dala miliyan biyar ga duk wanda zai bada bayanan da zasu kai ga kama Adnani.
Jami’an gwamnati a Washington sun shaidawa Muryar Amurka cewa, amurka ta gano manyan kungiyar IS da dama a lardin Aleppo, sai dai basu bada tabbacin ko Adnani na daya daga cikinsu ba.