A wata takardar bayani, Ma'aikatar Tsaron Rasha ta ce jiragen yakin Rasha sun hallaka mayakan ISIS wajen 40, ciki har da Abu Muhammad al-Adnani, a wani hari na ruwan bama-bamai daura da lardin Aleppo ranar Talata. Wani babban jami'in tsaro ya gaya ma Muryar Amurka cewa wannan ikirari na Rasha wani sabon yinkuri ne na sake yada bayanan karya.
Jami'in ya ce an yi ta sa ido kan al-Adnani na wani tsawon lokaci, kuma an kashe shi ne a wani harin jirgin sama da aka kai kan wata mota daura da Washiya, wani kauyen da ke arewa da birnin Aleppo.
Da kanta kungiyar ISIS ta ba da sanarwar mutuwar Abu Muhammad al-Adnani ranar Talata, da cewa an hallaka shi ne yayin da ya ke duba shirye-shiryen kai farmakin kawo karshen matakan soji da aka daukawa kan birnin Aleppo.