Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Kira Ga Turkiyya Ta Mayar Da Hankali Kan Yaki Da ISIS


Sojojin Turkiyya
Sojojin Turkiyya

Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter, ya yi kira ga kasar Turkiyya da ta mai da hankali kan yaki da ISIS, a maimakon raba hankalinta wajen fada da dakarun Kurdawa masu alaka da Amurka, wadanda su ma yaki su ke yi da kungiyar 'yan ta'addar ISIS a Siriya.

Sojojin Turkiyya da 'yan tawayen Siriya masu dasawa dasu sun shiga rana ta shida a gwagwarmayarsu ta fatattakar mayakan ISIS da Kurdawan YPG, wadanda su ke cikin dakarun karfafa dimokaradiyyar Siriya da Amurka ke goya ma baya, daga garin Jarablus da kewaye da ke wajejen kan iyakar Siriya da Turkiyya.

"Amurka ta nuna masu matukar goyon baya, kuma har yanzu ta na goyon bayan matakin soji da su ke daukawa kan ISIS da kuma duk kokarin da su ke yi na kwace yankin da ke wajejen Jarablus da kan iyakar da kuma bangaren yamma, amma banda kudancin Jarablus," in ji Carter ga manema labarai a hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon jiya Litini.

Kwanan nan dakarun Kurdawa su ka taimaka wajen fatattakar mayakan ISIS daga garin Manbij, mai tazarar kilomita 40 kudu da garin Jarablus kuma kilomita 30 yamma da kogin Euphrates.

Amurka ta ce dakarun Kurdawa na YPG sun ba da tabbacin cewa za su janye zuwa gabashin kogin da zarar an kammala kakkabe ISIS daga Manbij. Carter ya fadi jiya Litini cewa dakarun "za su janye kuma gabas za su yi," kuma Amurka Amurka na kokarin ta bayyana ma Turkiyya inda rukunonin dakarun SDF su ke, don a kau da wasu arangamar kuma a gaba.

XS
SM
MD
LG