Lokacin da suka sa hannu kan wata yarjejeniya akan daidaita lamuran da malaman ke korafi a kai sai kungiyar malaman ta fitar da sanarwar janye shirin yajin aikin da ta so ta fantsama ciki a wannan makon.
Gwamnatin kasar ta dauki alkawarin shafewa malaman hawayensu.
Sakataren kungiyar malaman Malam Sha'aibu Danbaji, jigo a kungiyar malaman ya yi karin bayani. Yace an kafa kwamiti na musamman da zai yi aiki akan albashin malamai zai kuma kammala aikinsa nan da karshen watan Mayu. Gwamnati ta dauki alkawarin biyan basukan da malaman suke binta. Gwamnati zata cigaba da biyan alawus alawus a karshen watan Mayu. Malaman da aka dauka aiki wajen shekaru biyu da suka wuce za'a daidaita lamuransu watan Yuni.
An cimma yarjejeniyar ne a lokacin da malaman da suke kwantiragi suka yi barazanar afkawa cikin yajin aikin kwanaki biyu a duk fadin kasar. Malaman sun yi korafin rashin samun albashi a kan lokaci da dai wasu dalilai kuma. Sun zargi hukumomi da sabawa alkawuran da suka dauka da can.
Ministan ilimi na matakin firamare Dauda Marte da yake bayani akan yarjejeniyar ya jawo hankulan mutane inda yace su duka a zauren 'ya'yan talakawa ne. Halin da makarantun gwamnati ke ciki lamari ne da yakamata ya dauki hankalin kowa. Kowa nada gudummawar da zai bayar domin a fitar da makarantun daga halin tagayyara.
Ga karin bayani.