Jami'an tsaron sun kama motar ne a garin Durku dake kan iyakar jamhuriyar Nijar da Libya daga hannun masu safarar miyagun kwayoyin.
Muggan kwayoyin masu safararta sun daukota ne daga tarayyar Najeriya suka biyo da ita cikin Nijar domin tsallaka da ita cikin kasar Libya watakila ma su arce da ita zuwa kasashen turai.
Malam Muguni Ibrahim jami'in 'yansanda mai kula da harkokin bincike a garin Agades ya yiwa manema labarai karin bayani. Yace sun samu ganyen wiwi kilo dari da arba'in da bakwai da hodar ibilis dubu saba'in da dai sauransu.
Manyan askarawan Nijar dake yankin Agades sun halarci bikin gabatar ma 'yan jarida kayan da aka kama kuma nan take alkali ya shigar da kara da sunan gwamnatin Nijar a babban kotun Agades.
Shi ma Malam Dubu Nuhu ya yiwa manema labarai karin bayani. Yace aikin da 'yansanda suka yi abu ne da suka ji dadinshi. Ya kira jama'a su san abubuwan da 'yansanda suka kama kana su dinga taimakon 'yansandan koda zasu ga wani abu kamar haka ana ratsawa dashi cikin kasar Nijar.
Ga karin bayani.