Kalaman na Osinbanjo, wanda ya wallafa a dandalin Twitter a daren Laraba 21 ga watan Oktoba, su ne na farko daga bangaren shugabannin kasar game da harbin da aka yi ranar Talata 20 ga watan na Oktoba a jihar Legas.
Shugaban kasa Muhamadu Buhari, wanda ya yi magana sosai ba akan zanga-zangar da ke mamaye kasarsa, bai ambaci harbe-harben da aka yi a Lekki ba a wata sanarwa da ya fidda jiya Laraba amma ya yi kira da a kwantar da hankali kuma ya yi alkawari yin garanbawul a tsarin ‘yan sanda.
Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa da kasa ta Amnesty International a wani rahoton da ta fidda ranar Laraba, ta ce mutune 38 suka mutu a ranar Talata kuma akalla mutune 56 suka mutu a cikin makonni biyu a zanga-zangar neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi, da aka fi sani da SARS, wacce kungiyar ta Amnesty ta zarga da azabtarwa da kuma kisa.
A makon da ya gabata gwamnatin kasar ta soke rundunar amma hakan bai hana zanga-zangar ba, inda wasu suka bijire wa dokar hana fita da aka sanya ranar Laraba, abinda ya haddasa karin harbe-harbe, amma ba a samu rahoton kisa ba.
Facebook Forum