Biyo bayan kiraye-kiraye da ake cigaba da yi a Najeriya, don kawo karshen zanga-zangar da ta kwashe fiye da mako guda ana yi a kasar, 'yan Majalisar Taryyar Najeriya sun shiga kiran Buhari da ya yi bayanin mafita.
'Yan Majalisu sun jaddada bukatar da ke akwai ga Shugaban kasa na yayi jawabin matakan gaggawa da zai dauka akan kudurorin da masu zanga-zanga suka gabatar, tare da yin kira ga 'yan Najeriya da su yi amfani da kafofin Shari'a don magance rikice-rikice.
Bugu da kari, 'yan majalisun sun yi kira ga dukan bangarorin gwamnati da su cigaba da tabbatar da manufofin sake fasalin zamantakewar al'umma, wanda zai daga darajar rayuwar mutane.
Sanata mai wakiltar jihar Neja ta gabas Mohammed Sani Musa, ya ce mambobin babban Kwamitin jam'iyyar APC a Majalisar Dattawa sun sake nazarin zanga-zangar, inda suka cimma matsaya cewa gwamnati ta hanzarta sake nazarin shirin da zai taimaka wa matasan kasar, su samu abun yi a cikin shirin ta N-power da shirin tallafi na kananan sana'o'i, hakan zai taimaka musu wajen iya dogaro da kansu.
Ganin cewa su ne tushen zanga-zangar nuna bacin ran su, Sanata Sani Musa ya kara da cewar, sun yi amanna da bayanan da Sufeto Janar na 'yan sanda ya yi, cewa duk wadanda aka kama suna barnata dukiyar wasu za a gurfanar da su a gaban kuliya.
A nashi nazarin, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Jibiya, Kaita a Jihar Katsina, Sada Soli Jibiya ya ce lallai majalisa ta yi hobbasa wajen ganin Shugaba Buhari ya yi gaggawar daukar matakin magance matsalar da kasa ta samu kanta a ciki, saboda haka ya fito da wata doka da kundin tsarin mulki ya bashi hurumin yi wadda aka fi sani da Executive Order a Turance.
Jibiya na ganin cewar idan Buhari yayi amfani da wannan karfin na Shugaba Mai Cikakken iko, ana iya samun saukin matsalar. Ya ce ya kamata mutane su san cewar Majalisar kasa na iyakar kokarinta na ganin an samu maslaha kan wannan al'amarin.
Dukan kudurorin sun samu goyon bayan daukacin 'yan majalisar da suka halarci zaman Majalisun biyu.
Ga rahoton Madina Dauda a cikin sauti:
Facebook Forum