Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Bukaci A Kwantar Da Hankali A Daina Zanga-zanga


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari mai cike da kiraye kirayen a kawo karshen zanga-zanga a dubi lamarin cikin natsuwa, na dauke da muhimman sakonni ga duka bangarorin.

Shugaban kasa Muhammdu Buhari, yayi kira da a kwantar da hankali, a kuma zauna lafiya a kasa, ya kara da cewar, gwamnati tana nan tana aiki akan koke koken al'umma na neman a yi wa dokokin hukumar ‘yan sanda gyarar fuska.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wata sanarwar da mai bashi shawara kan harkar labarai Femi Adesina ya fitar, ya jaddada cewar gwamnatin Buhari a shirye take ta kawo tsare-tsare masu ma'ana a bangaren ‘yan sanda.

Shugaba Buhari yayi maraba da kwamitin bin bahasin ayyukan rundunar ‘yan sanda a jihohi 13, wanda majalisar zartarwa ta bada umurnin a yi don bin kadin mutane da ‘yan sanda suka ci zarafinsu a daukacin kasar.

Ya zuwa yanzu jihohin da suka kafa wadannan kwamitin binciken sun hada da jihar Legas, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Ondo da Akwa Ibom. Shugaba Buhari yana goyon bayan wadannan jihohin akan wannan aikin, da kuma ganin an hukunta wadanda suka ci zarafin jama’a a fadin kasar.

Kwamitin zartarwa karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yayi zama a ranar 15 ga watan Oktoba, ta 2020, kana ya cinma matsaya akan kafa wadannan kwamitocin, don bincikar ire-iren ayyukan da ‘yan sanda suka yi na cin zarafin jama’a a kowane mataki.

An kashe mutane gwammai jiya Talata a birnin Legas, Abuja, Kano, Oyo, Ogun da Filato, inda dubbai kuma suka samu raunuka, biyo bayan zanga-zangar kawo karshen hukumar SARS. Wadanda abun ya shafa sun hada da jami’an tsaro, da masu goyon bayan soke rundunar da wadanda basu goyon bayan hakan, haka kuma da jama’a wadanda basu ji ba, basu gani ba.

A lokacin bata kashi a tsakanin bangarorin biyu an rusa gine-gine, shaguna da kona motoci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG