Mai alfarma ya furta hakan ne lokacin da ya karbi mubaya'ar sabon Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a fadar sa.
Dangantaka tsakanin Cibiyar daular Usmaniya da masarautar Zazzau ta samo asali tun lokacin da Shehu Usmanu Danfodiyo ya baiwa Malam Musa tuta ta jaddada addinin musulunci a masarautar Zazzau.
Tun daga wannan lokacin duk wanda aka nada Khalifa a wannan masarautar sai yayi mubaya'a ga khalifan shehu Usman Danfodiyo domin jaddada wannan dangantakar.
an-nada-alhaji-ahmad-nuhu-bamalli-a-matsayin-sarkin-na-19-na-zazzau
gwamna-nasiru-el-rufai-na-jihar-kaduna-a-najeriya-ya-nada-magajin-garin-zazzau-alhaji-ahmad-nuhu-bamalli-a-matsayin-sarkin-na-19-zazzau
hira-da-mai-martaba-sarkin-zazzau-alhaji-ahmad-bamalli
Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli shima bai yar da gado ba domin ya je Sakkwato inda yayi mubaya'a ga sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar wanda shine Khalifan mujaddadi Danfodiyo. Ya baiwa khalifan tabbacin goyon baya da biyayya ga cibiyar ta daular Usmaniya. Ya kuma shedawa Sarkin musulmi cewa babu matsala a masarautar Zazzau kuma an tsayar da ranar 9 ga watan Nuwamba a zaman ranar da za a mika masa sandar girma.
Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya nuna gamsuwa da wannan zumunci mai dadadden tarihi da Sabon sarkin ya jaddada ya kuma yi kira gareshi da yayi adalci ga kowa domin kowa nasa ne.
Wannan ziyarar da Sabon sarkin Zazzau na zuwa ne lokacin da daya daga cikin yan masarautar ta Zazzau Iyan Zazzau Bashir Aminu ya garzaya kotu yana kalubalantar nadin Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli a zaman sarkin na Zazzau.
Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti;
Facebook Forum