Kasancewar yanayin rashin tabbas da ke a jihar Legas, da ma Najeriya baki daya, gwamnan jihar LEGAS, Babajide Sanwo-Olu, ya bada umurnin dakatar da duk wasu ayyukan gwamnati a jihar na tsawon kwanaki uku.
Ayyukan da suka shafi fannin tsaro da masu gudanarwa kawai za su cigaba, cikin umurnin za a saukar da tutar kasa a duk ofisoshin gwamnati zuwa kasa, na tsawon wadannan kwankin 3. Gwaman ya sanar da hakan a lokacin da yake magana ta kafar talabijin yau Laraba.
Gwamnan ya umurci a kafa kwamiti mai mutane 5 da za su binciki abun da ya faru, kana wanda zai jagoranci kwamitin zai zama soja wanda ya yi murabus a mutakin Janar. Ya ce rahoton kwamitin kuma za a gabatar da shi ga Shugaban kasa nan da makonni biyu.
Ya kara da cewa “Tabbas ina iya cewa muna samun nasara tare, duk da cewer abubuwa na tafiyar hawainiya, bisa dalilin rashin shugabanci ta bangaren masu zanga-zangar kawo karshen rundunar ta SARS.”
Facebook Forum