Ministan harkokin cikin gida na Kenya yayi gargadin cewa za a iya kama shugaban adawa Raila Odinga dangane da bikin rantsar da shi a matsayin “shugaban mutane” ranar Talata. A halin da ake ciki hukumomi sun ce an hana gidajen yada labaran cikin gida yada bikin na ranar Talata har sai an kammala bincike.
Ministan cikin gida Fred Matiang’i ya ce bikin nadin Raila Odinga, “wani yunkuri ne na hambarar da gwamnati.”
Biyo bayan wani taron manema labarai da ministan yayi jiya Laraba, gidajen yada labaran kasar har sun rawaito cewa an kama a kalla mutum guda, lawya kuma ‘dan majalisar adawa wanda ya tsaya tare da Odinga lokacin da ake rantsar da shi.
Wani masanin shari’a ya fadawa Muryar Amurka cewa abu ne mai wahala ga hukumomi su kama Odinga, saboda a bikin ba a rantsar da shi ba a matsayin shugaban kasar Kenya ba. Yanzu haka a shafinsa na Twitter ana bayyana shi da sunan “mai girma”
Facebook Forum