Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Kara Fadada Takunkumin Makamai a Kan Afrika ta Tsakiya


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata ya sabunta takunkumin makamai a kan jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da shekarar guda, kuma yayi karin wani ma’aunin da zai kai ga karin sabbin takunkumai.

Kudurin da Faransa ta gabatar, ya samu amincewar bakin dayan wakilan kwamitin.

Baicin karin lokacin takunkumin, kudurin ya kuma yi Allah wadai da amfani da addini da kabilanci wurin iza tashin hankali. Yace duk wanda ya aikata irin wannan laifin zai fuskanci jan kunne.

Rura wutar tashin hankali wata babbar annoba ce ga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya kuma shine ya haddasa tashin hankalin da yayi sanadiyar jikatta fararen hula da dama da ma wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, inji wakilin Faransa a kwamitin sulhun Francois Delattre. Yace kasar Afrika ta Tsakiya ba zata zauna lafiya ba, muddin za a ci gaba da rura wutar tashin hankali kuma kwamitin sulhun MDD zai dauki alhakin kulawa da hakan.

Kasar Afrika ta Tsakiya ta fada cikin tashin hankali, tun bayan da yan tawayen Musulmi suka hambarar da shugaban kasar Krista.

Mabiya addinin Krista kuma sun maida martani, wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga dukkan bangarorin kana dubban yan gudun hijiran Musulmi suka suka arce zuwa Kamaru da Chadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG