Yan tawayen kungiyar adawa a Sudan ta Sudan People's Army in Opposition (SPLA IO), masu biyayya ga Riek Machar sun ce sun mika sojojin gwamnati 15 ga kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, a karamin filin saukar jiragen sama na KoloPach, a jihar Jonglei.
Mukaddashin mai Magana da yawun kungiyar yan tawayen ta SPLAIO Col. Lam Paul ya fada a jiya Lahadi cewa, goma sha daya a cikin sojojin gwamnatin sun ki yarda su je birnin Juba, gudun kwamandodjinsu zasu musguna musu.
Kungiyar yan tawayen sun yi marhabi da shawarar sojojin kuma suka basu yancin zama tare da mutanen da suka rasa matsuganansu a cikin jihar.
Wannan dai karo na uku da kungiyar yan tawayen SPLAIO ta nuna biyayya ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanyawa hannu a cikin wata Disemban bara, yayin da wasu bangarori na wannan yarjejeniyar, har yanzu basu fara mutunta ka’idodin ta, inji Gabriel
Kungiyar kasa da kasa ta Red Cross bata tabbatar ko karyata wannan batu na mika sojojin ba, sai dai tace ba zata yi wani bayani a kan tattaunawa da tayi da bangarorin ko kuma nasara da ake samu.
Facebook Forum