A cikin garin Maradi masu injinan nika sun tsayar da aiki na yini guda da zummar bayyana matsalar da suke fuskanta sabili da karin kudi da kamfanin wutar lantarki ya yi.
To sai dai karin na da nasaba da sabuwar dokar biyan haraji da gwamnatin kasar ta kafa ta kuma fara aiki farkon shekarar nan.
Malam Isaka Boi sakataren kungiyar masu nika a Maradi ya ce tun karfe shida na safe yake zagayawa ya ga gidan nika da yake aiki amma babu ko daya. A cewarsa dole ne suka shiga yajin domin babu abun da zasu iya yi.
Muryar Amurka ta garzaya zuwa kamfanin wutar lantarki ta ji ta bakinsu. Alhaji Mamman Abdulrahaman shugaban kamfanin ya ce abun ya fi karfin kamfanin saboda dokar kasa ce ta kara haraji.
A bangaren talakawa, masu kosai, masu sarafa fura zuwa masu gidaje dake kai nikan abun da zasu ci sun ce yanzu ba kosai kuma babu tuwo. Wani ya ce tunda safe ake yawo a samu inda za'a nika masa masara amma babu.
Ga rahoton Chuaibu Mani da karin bayani
Facebook Forum