Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Liberiya Ya Ragewa Kansa Albashi


Shugaba George Weah, lokacin da yake rantsuwar kama aiki
Shugaba George Weah, lokacin da yake rantsuwar kama aiki

A kokarin ganin tattalin arzikin kasarsa ya bunkasa, shugaban Liberiya George Weah ya rage ma kansa albashi da wasu alawus-alawus

Shugaban kasar Liberiya, Geoge Manneh Weah, ya bayyana cewa ya rage yawan albashin sa dama wasu alawus-alawus dinsa, tare da fatan ‘yan majalisar dokokin kasar su ma zasu bi sahu.

A bisa tsari dai shugaban kasar Liberiya zai samu albashin da zai kai dala miliyan 4 ne a shekara.

Shugaban ya bayyana hakan a lokacinda yayi wa kasa jawabin farko a ranar littinin.

Shugaba Weah yace ya gaji tattalin arzikin kasa dake da rauni saboda faduwar darajar kudin kasar, da matsalar hauhawar farashin kayayyaki da abin masarufi, da rashin aikin yi tare da karancin kudi a lalitar gwamnati dake kasar waje.

Wani batu da shugaban yace zai ba wa muhimmaci shine yadda ‘yan kasar suka dade suna neman 'yancin zama ‘yan kasa biyu.

Shugaba Weah yace ana yi wa kowanne dan kasa maraba da dawowa gida koda kuwa yana da iznin zama dan wata kasa ce dabam da kasar Liberiya, muddin dai shi dan asalin kasar ne.

Haka kuma yace gwamnati zata baiwa abubuwa hudu muhimmanci, wadanda suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasa tare da samar da aikin yi da kuma ganin zaman lafiyar dake kasar yaci gaba da dorewa sai kuma tafiyar da ayyukan gwamnati ba tare da boye-boye ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG